Jam iyar APC ta lashe zaben shuwagabanin kananan hukumomi a fadin Jahar Gombe.

 




Jam iyar APC Mai Mulki a jahar Gombe ta lashe dukkanin kujerun shuwagabannin kananan hukumomi 11 dake fadin jahar harma da kansiloli 114 a jahar ta Gombe.



Da yake sanar da sakomokon zaben shuwagabanin kananan hukumomi da akayi a fadin jahar Saidu Shehu Awak yace kansiloli 114 sunyi nasaran cin zaben ne batare da abokan hamaiyaba, hakama jam iyar tayi nasaran cinye dukkanin shuwagabanin kananan mukumomi 11 dake fadin jahar.



A cewarsa a kalka jam iyu biyar ne suka shiga zaben da suka hada da PDP. ANPP. YPP. ZLP da Kuma jam iyar Accord.




Jami in tattara sakamokon zaben ya godewa jam iyu da suka shiga zaben dama Al umma jahar bisa yadda suka bada hadin Kai domin yadda aka gudanar da zaben lafiya.




Da yake magana a madadin jam iyu da suka shiga zaben shugaban  kungiyar dake shiga tsakanin jam iyu IPAC Kuma shine shugaban. Jam iyar Accord a jahar Gombe Alhaji Muhammad Adamu ya amice da Kaye da yasha tare da taya murna ga jam iyar APC bisa nasara da ta samu ya Kuma baiyana farin cikinsa dangane da yadda jam iyarsa tazo na biyu.



A ranan asabar da ta gabata ne dai aka gudanar da zaben shuwagabanin kananan hukumomi da kansiloli a fadin jahar ta Gombe.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE