Kungiyar mafarauta na samun kwarin gwiwar yakan yan bindiga.

 



Kungiyar mafarauta na samun goyon bayan hukumomin tsaro domin yakan masu tada kayan baya a tsakanin Al umma baki Daya.


Muhammed Adamu Sarkin yakin mafarautar jahar Adamawa ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai Jin kadan da nada shugaban kungiyar mafarauta na yankin arewa masau gabas na riko da aka gudanar a karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa.



Muhammed Adamu yace saboda irin gudumawa da suke bayarwa ne yasa hukumar tsaron farin kaya wato DSS da hadin kan fadar shugaban kasa suka taimaka masu da wasu makamai da zasu tunkari yan bindigan wadanda keyiwa zaman lafiya barazana.


Sarkin yaki na mafarauta ya baiyana cewa sun bada gudamawa sosai wajen yakan Yan bindiga kama daga jahar Adamawa dama sauran jihohi irinsu Borno, Yobe, inda Kuma a yanzu suna yankin Abuja a wani mataki na dakile matsalar tsaro baki Daya.


Muhammed Adamu ya nuna farin cikinsa dangane da nada Modibbo Idris Usman Tola a matsayin shugaban kungiyar mafarautan yankin arewa masau gabas na riko tare da Kira da abaiwa sabon shugaban   hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran yakan Yan bindiga.



Ya Kuma yabawa hukumomin tsaro da suka hada da DSS da rundunan yan sanda bisa hadin Kai da goyon baya da suke baiwa mafarauta Wanda hakan ya taimaka kwarai wajen yakan Yan bindiga.


A cewarsa kungiyar tasu ta mafarauta a shirye take tacigaba da baiwa hukumomin tsaron hadin Kai da Kuma bin Ka idodin aiki domin ganin an Kai ga samun nasara.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.