Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan tsaro a yankin Mubi.

 



A kokarinta na takawa masu aikata laifuka birki rundunan yan sandan jahar Adamawa ta gudanar da taro na musamman da sarakunan gargajiya, shuwagabanin addinai, dama masu ruwa da tsaki domin Samar da hanyoyin yiwa tukan janci.



Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya ziyarci tare ta shirya tattaunawa da Al umma dake taimakawa Yan sanda domin yin aiki tare wajen magance matsalar Yan shila, masu garkuwa da mutane, Yan fashi da makami, naratin shanu da  dai sauran aikata laifuka a yankin baki Daya.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola.




Kwamishinan ya gana da masu ruwa da tsaki, da PCRC, shuwagabanin Al umma, mafarauta, Yan Sa Kai,tare da wakilain makiyaya Dana manoma Yan kasuwa da Kuma DPO na ofishoshin Yan sanda da suke kananan hukumomin Mubi ta arewa, Mubi ta kudu, Maiha, Michika,, Mugulvu,  mararraba Mubi, Madagaki, Uba hildi domin Samar da dabaru wajen magance dukkanin kalubalen tsaro a yankin dama jahar baki Daya.



Harwayau kwamishinan ya kirayi manyan Jami an sanda dake yankin dama sauran hukumomin tsaro da suyi dukkanin abinda suka dace domin ganin anbi doka da oda.



Ya Kuma Yi gargadi cewa  kada Jami in dan sanda ya kuskura aka mashi da yin ba daidaiba saboda haka yaksance Mai nuna da a a Koda yaushe.



A jawabinsa sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya yabawa rundunan yan sandan bisa shirya wannan taro tare da nuna matukan goyon bayansa dangane da matakin rundunan ya Kuma godewa kwamishinan bisa ziyartan fadarsa da yayi.



Kwamishin ya Kai ziyaran ne tare da rakiyar manyan Jami an ysandan da suka hada da mataimakin kwamishinan Mai kula da bincike DCP Dankaro U Ayuba da DCP Fakeye Olubunmi Olubode kwamnadan rundunan yan sandan kwantar da tarzoma ta 14 dake nan Yola. da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE