Majalisar dokokin jahar Adamawa ta tabbatar da sunan HammaJumba Gatugel a matsayin kwamishina a jahar Adamawa.

 



Majalisar dokokin jahar Adamawa ta tantance tare da tabbatar da HammanJubba Gatugel a matsayin kwamishinan da zai kasance memba a majalisar zantarwan jahar Adamawa.




Tabbatar da sunan Hamman Jbba ya biyo bayan amincewa da kwamitin majalisar tayi a zamanta na ranan litin karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jahar ta Adamawa Hon. Bathia Wesley.



Hamman Jubba Gatugel ya fito ne daga karamar hukumar Mayo Belwa dake jahar Adamawa. Kuma kafin tabbatar dashi a matsayin kwamishina shine shugaban kungiyar ma aikatan kananan hukumomi a Najeriya NULGE shiyar jahar Adamawa, Wanda Kuma kawo yanzu gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zai bashi damar kasancewa a cikin membobin majalisarsa.



Bayan an tantanceshi tare da tabbatar dashi sai kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa ya murci a kawun majalisar da sanar da gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri matakin na majalisar.




Da yake zantawa da manema labarai Jin kadan da tantanceshi a matsayin kwamishina HammaJumba Gatugel ya godewa gwamna Ahmadu Fintiri da ya bashi damar kasancewa zaiyi aiki a karkashin gwamnatinsa Kuma da yardan Allah ba zai bashi kunyaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE