Majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa ta taimakawa Yan kasuwa Yola da kudi dubu Dari biyu da hamsin.





 An shawarci Yan kasuwa da sukasance masu gudanar da harkokinsu bisa tsorron Allah da Kuma bin dokokin addinin musulunci a harkokin kaauwancinsu domin samun cigaban kaauwancinsu yadda ya kamata.


Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne ya bada wannan shawara a lokacinda ya jagoranci tawagan majalisar zuwa jajantawa yan kasuwar yola da iftala I gobara da ta shafa.


Alhaji Gambo Jika ya Kuma kirayi Yan kasuwa da sukasance masu maida dukkanin lamuransu ga Allah madaukakin sarki tare Kuma da yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar.

Alhaji Gambo ya Kuma kirayi gwamnatoci da masu hanu da shuni harma da kungiyoyi da su kawowa Yan kasuwan musammanma wadanda iftalai ya shafa daukin gaggawa domin rage musu yawan asara da sukayi sakomokon gobara.


A cewarsa dai taimakawa Yana da muhimmanci saboda wasu sun rasa dukkanin abinda suke dashi sakomokon gobaran saboda haka in ba a Kai musu daukina to zasu shiga wani yanayi na matsalar rayuwa.


Shima anashi jawabi shugaban kungiyar Yan kasuwan arewacin Najeriya hada da birnin tarayya Alhaji Muhammadu Ibrahim 86 ya yabawa majalisar Addinin musulunci bisa wannan taimako da suka kawowa yan kasuwa Wanda hakan zai rage radadin wahalar da zasu iya shiga.sakomokon gobaran.


Ya Kuma kirayi sauran kungiyoyi da Suma sukoyi da majalisar ta addinin musulunci wajen taimakawa wadanda iftala I ya shafa. Musammanma gwamnati.


Majalisar harkokin addinin musulunci dai ta taimaka wa yan kasuwar da kudi nera dubu Dari biyu da hamsin. Wato N250,000.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE