Rundunan yan sandan jahar Adamawa Tasha alwashin takawa masu aikata laifuka birki a fadin jahar.

 



Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin kawo karshen aikata laifuka a fadin jahar ta Adamawa baki Daya.


Rundunan ta bakin kakakinta SP Suleiman Yahaya Nguroje yace rundunan baza tayi kasa a gwiwaba wajen daukan dukkanin matakai da suka dace domin dakile matsalar.


SP Suleiman Yahaya Nguroje yace rundunan ta kimtsa tsaf domin kama tare da hukunta duk Wanda aka samu da aikata laifuka.



Saboda haka nema rundunan ta Samar da runduna ta musamman domin yaki da ta addanci.a fadin jahar.


Kakakin rundunan yan sandan ya Kuma kirayi daukaci Al ummar jahar da cewa da zaran sunga abinda basu yarda da suba su gaggauta Kai rahoton zuwa ofishin Jami an tsaro domin daukan mataki a Kai.


Domin a cewarsa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin jama a saboda haka akwai bukatan Al umma su baiwa hukumomin tsaro hadin Kai da goyon baya domin samun nasara da zaman lafiya a fadin jahar baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE