Shugaban Darikar Katilika a jahar Adamawa ya bada shawaran yiwa shuwagabani da kasa adu a.
Duba da yanayi da ake ciki an shawarci Yan kasuwa da sukasance masu sausauci a harkokin kaauwancinsu domin samun damar bunkasa harkokinsu dama tattalin Arzikin kasa baki Daya.
Shugaban Darikar katilika a jahar Adamawa Rev. Bishop Dami Manza ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Rev. Dami Manza yace a yanzu farashin dala ya sauka to amman har yanzu ba aga saukar kayakiba a kasuwannin saboda haka Yana da muhimmanci yan kasuwa sukasance masu taimakawa da Kuma kautatawa a harkokinsu na kasuwanci Wanda hakan zaitaimaka wajen samun aknarkar kasuwancinsu a koda yaushe.
Rev. Manza ya kirayi Yan Najeriya da sukasance masu yiwa shuwagabanin fatan Alheri da Yi musu adu a tare da basu hadin Kai da goyon baya Wanda a cewarsa hakan ne zaibasu damar gudanar da aiyukan cigaban Al umma baki Daya.
Rev. Ya Kuma shawarci Al umma da su nisanta kansu da aibata shuwagabanni Mai makon haka ya kamata suyi musu adu a domin Allah ya taimakesu wajen aiyuka dama kare rayuka da dukiyoyin jama a.
Bishop Manza yace duk da cewa shuwagabanin suna iya kokarinsu to su Kara kaimi wajen tallafawa jama a domin rage musu wannan radadin wahalar rayuwa da ake ciki.
Ya Kuma ja hankalin shuwagabanin da maida hankali wajen kula da walwalan Al umma da Kuma tausaya musu a Koda yaushe.
Bishop ya shawarci Yan Najeriya da sukasance masu yin adu o I domin Neman taimakon Allah wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan.
Comments
Post a Comment