Wanda ake zargi da satar mota ya shiga hanu a jahar Adamawa.
A yanzu haka rundunan yan sanda a jahar Adamawa tana tsare da wani mai suna Ibrahim Ali da ake zarginsa da satar karamar mota Kiran sitalen Mai dauke da nimbar rijista JMT 317 RA.
An samu nasaran kama Wanda ake zargin ne a shingen binciken ababen hawa dake Ngurore Kuma ya tabbatar da aikata lafin indama yace ya saci motar ce a wani wuri dake cikin garin Jimeta dake karamar hukumar yola ta Arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwa ta baiyana cewa kwamishinan yan sanda jahar Adamawa Dankombo Morris ya kirayi Al umma musammanma wadanda aka Wanda aka satar masa mota da yaje ofishin yan dake Nguroje da yayi bayani domin ya karbi kayansa.
Comments
Post a Comment