Yan Sanda a jahar Adamawa sun daura damaran yakan masu aikata laifuka a fadin jahar.

 



Rundunan yan sanda jahar Adamawa tace tana kan bakanta na cigaba da yaki da masu kawowa Al umma matsala a harkokinsu na yau da kullum a fadin jaha.


Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


Sanarwan ta baiyana cewa rundunan ta samu nasaran cafke masu aikata laifuka a wani samame da ta Kai a manoyan masu aikata laifuka a wurare da suka hada da mahadar Geriyo, da Doubeki, Jambutu Aso Rock, bayan makarantar Ramat,da Kuma hanyar Sama dake total Wanda a yanzu haka tana tsare da mutane 49 ciki harda mata biyu. Kuma kawo yanzu ana cigaba da bincike domin tabbatar da anyi adalci.


Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya tabbatarwa Al ummar jahar Adamawa cewa rundunan bazatayi kasa a gwiwaba zataci gaba da yin dukkanin abinda suka wajaba domin yaki da bata gari a fadin jahar.


Rundunan ta kirayi Al ummar jahar da sukasance masu taimakawa rundunan da bayanai sirri da Kuma Kai rahoton dukkanin abinda basu amince da Shiba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE