An bukaci gwamnati da ta sanya ido kan harkokin kwale kwale domin magance hatsari da ake samu akan ruwa.




 An shawarci Al umma da su kaucewa zuwa gogi barkatai in ba da wani daliliba domin kaucewa shiga hatsarin da zaiyi sanadiyar asaran rayuka.


Abubakar AbdulRazaq shugaban kungiyar manoma yankore Kuma sarkin ruwan Geriyo ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Abubakar AbdulRazak yace bai daceba mutane su rinka mu amala da kan ruwa musammanma in mutu bai da wata halaka da ruwa. Tare da Kiran masu amfani da kwale kwale da kaucewa diban kaya ko mutane fiye da kima a cikin kwale kwale domin kaucewa aukuwar hatsari.


Su Kuma Al umma sukasance masu sanin Wanda zai tukasu a kwale kwale domin tsira da rayuwarsu da Kuma lafiyarsu a Koda yaushe.


Ya Kuma shawarci iyaye da sukasance masu sanya ido akan yaransu tare da hanasu zuwa gogi a wani mataki na kaucewa asaran rayuka.


Abubakar ya shawarci gwamnati da ta shiga tsakani ta sanya ido da maida hankali kan matuka kwale kwale da Kuma taimaka musu da kayakin kwale kwale masu ingancin, Wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen kawo karshen yawan hatsari da ake samu akan ruwa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE