An bukaci maniyata da sukasance suna halartan bita da ake musu.

 



A yayinda ake shirye shiryen aikin Hajjin wannan shekara an shawarci maniyata  da su kasance masu zuwa bita a Koda yaushe domin ganin sun samu saukin gudanar da aikin Hajji cikik tsanaki ba tare da matsalaba.


Jami in tsare tsaren aikin Hajjin karamar hukumar Madagaki. Kuma Uban dokan Gulak Alhaji Suleiman Yusuf ne ya yi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a wurinda ake gudanar da bita a makarantar G R A dake Jimeta a karamar hukumar yola ta Arewa a jahar Adamawa.


Alhaji Suleiman Yusuf yace duk da cewa an samu matsàloli musammanma Karin kudi da hukumar Saudiya tayi amman sun fadakar da maniyatan da su rungumi lamarin a matsayin kaddara. Saboda haka kawo yanzu komai Yana tafiya dai dai ba tare da matsalaba.


Alhaji Suleiman yace lamarin Kam baiyi dadiba Amna hakuri shine maganin matsalar saboda haka nema suke Jan hankalin maniyatan da sukasance masu hakuri a Koda yaushe.


Shima a jawabinsa Jam in tsare tsare aikin Hajji karamar hukumar yola ta arewa Alhaji Ya u Gambo yace saboda irin fadakarwa da sukeyiwa maniyatan nema. Maniyata ke fahintar duk abinda kanje kan komo.


Don hake nema yake kira ga maniyata da su maida hankali wajen zuwa bita Wanda a cewarsa hakan zaitaimaka musu wajen yin aikin hajjinsu yadda ya kamata.



Da yake magana dangane da bitan Mallam Muhammed Chibado Wanda shinema yake gabatarwa maniyatan bita yace sukam komai Yana tafiya dai dai ba tare da matsalaba ya dai ja hankalin maniyatan da su Kara kaimi wajen zuwa bitan domin ta haka ne zasu fahinci yadda aikin Hajji yake.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.