An ja hankalin maniyatan da sukasance masu bin dokokin aikin Hajji.

 





An shawarci maniyata musammanma Fulani da sukasance jakadu ma gari a lokacin aikin Hajji a kasar Saudiya domin kare martaban jahar Adamawa dama Najeriya baki Daya.


Shugaban kungiyar Sullubawa a jahar Adamawa Alhaji Bello Ardo ne ya bada wannan shawara a ganawa da yayi da manema labarai Jin kadan da kammala taro Wanda hukamar jindadin Alhazain jahar Adamawa tare da hadin gwiwar majalisar Addinin musulunci jahar Adamawa suka shirya Yola  dangane da wayarwa Al hazai Kai a yayin da ake daf da tashin maniyatan zuwa kasa Mai tsarki.


Alhaji  Bello Ardo yace Al umma Fulani mutane ne Wandanda aka sansu da biyayya saboda haka su cigaba da yiwa shuwagabanin biyayya da Kuma basu hadin Kai domin ganin sun gudanar da aikin hajjinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsalaba.


Alhaji Bello ya Kuma kirayi maniyata Al umma Fulani da sukasance sun sanya jahar Adamawa dama Najeriya cikin adu o insu a kasa Mai tsarki domin Neman taimakon Allah wajen wanzar da zaman lafiya a jahar dama kasa baki Daya.


Ya Kuma jinjinawa hukamar jindadin Alhazain jahar ta Adamawa bisa na mijin kokari da takeyi na ganin cewa maniyatan jahar Adamawa basu samu matsalaba a lokaci dama bayan aikin Hajji a wanna shekara.


Bello ya yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa na mijin kokari da yakeyi na kula da walwalan maniyata dake fadin jahar ta Adamawa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE