An rantsar da sabon kwamishinan sifiri a jahar Adamawa.
Gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya rantsar da sabon kwamishinan sifiri jahar Alhaji Hammajumba Gatugel.
Rantsarwan dai ya biyo bayan amincewa da sunansa a matsayin kwamishinan ne Wanda majalisar dokokin jahar ta Adamawa ta tantanceshi bayan gwamnan ya akewa majalisar sunanansa
A yayin rantsar da kwamishinan gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kirayi sabon kwamishin da ya gudanar da aiyukansa bilhakki da gaskiya domin samun cigaban ma aikatar ta sifiri dama jahar baki daya.
Gwamnan Fintiri ya Kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na gudanar da aiyukan cigaban jahar dama Al ummar jahar baki Daya.
Shima a jawabinsa sabon kwamishinan sifiri Hammajumba Gatugel ya godewa gwamna bisa wannan dama da ya bashi domin ya bada tashi gudamawa wajen cigaban jahar.
Ya Kuma yabawa gwamnan bisa aiyukan cigaba dayakeyiwa jahar Kuma a shirye yake ya baiwa gwamnan goyon baya da hadin Kai domin ganin ya cimma burinsa na gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Comments
Post a Comment