An yabawa gwamna Fintiri bisa aikin cigaban jahar.,,,,,,,,Kwamishinan Sifiri.,

 




A yayinda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ke cika shekara Daya akan Mulki a wa adi na biyu an yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa aiyukan cigaban jahar da yakeyi a Koda youshe.


Kwamishinan harkokin sifiri a jahar Adamawa Alhaji HammaJumba Gatugel ne yayi wannan yabo a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Alhaji HammaJumba Gatugel yace gwamna Ahmadu Fintiri ya taka rawan gani wajen gudanar da aiyukan daban daban na cigaban jahar da suka hada da hanyoyyi, kiwon lafiya, Ilimi, harkokin sifiri, tsaro, da dai sauransu.


A cewar Gatugel dai gwamnan yayai na mijin kokari wajen biyan albashin ma aikata Akai Akai ba tare da jinkiriba Wanda hakama cigaba ne matuka.


Saboda haka gwamna Fintiri ya gudanar da aiyukan inganta rayuwar Al umma da baza su musultuba a jahar Adamawa.


Da wannan ne HammaJumba yake kira ga daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu marawa gwamna Fintiri baya a Koda yaushe domin ya samu kwarin gwiwa cigaba da gudanar da aiyuka a fadin jahar.


Ya Kuma shawarci jama a da su cigaba da yin adu o I domin Samar da zaman lafiya da yiwa gwamnan adu a domin Neman Allah madaukakin sarki ya taimakeshi wajen cika burinsa na daga martaban jahar.


Gatugel ya tayar gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri murnan cika shekara Daya akan muki a wa adi na biyu. Tare da Yi masa adu ar fatan Alheri. 


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE