An yabawa gwamnatin jahar Adamawa bisa aiyukan cigaban jahar

 



An yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinta na aiyukan cigaban jahar.


Shugaban kungiyar Sullubawa ta kasa shiyar jahar Adamawa Alhaji Bello Ardo ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Alhaji Bello yace gwamnatin ta taka rawan gani a bangarori daban daban da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, tsaro, tattalin Arziki, hanyoyi, da dai sauransu.

Don haka nema kungiyar Sullubawa ke taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan cika shekara Daya akan Mulki a wa adi na biyu, Wanda ya gudanar da aiyukan cigaban Al ummar jahar ta Adamawa.


Alhaji Ardo ya shawarci daukin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu baiwa gwamnatin Ahmadu Umaru Finti hadin Kai da goyon baya, da Kuma Yi masa adu ar Allah ma daukakin Sarkin ya bashi damar cigaban da aiyukan cigaban jahar.


Ya Kuma tabbatar da cewa kungiyarsu a shirye take ta baiwa gwamna Ahmadu Umaru Finti goyon baya a Koda yaushe domin ganin ya samu nasaran gudanar da shugabancinsa yadda ya kamata ba tare da matsaloliba.


Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE