Ana cigaba da baiyana aiyukan cigaban jahar da gwamna Fintiri keyi..........Barista Sunday.

 



A yayinda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya cika shekara daya akan Mulki a zango na biyu an yabawa gwamnatinsa bisa na mijin kokari da takeyi na inganta rayuwar Al ummar fadin jahar.


Mashawarci na musamman akan harkokin Al umma Barista Sunday Wugira ne yayi wannan yabo a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa 


Barista Sunday yace gwamna ya taka rawan ganin wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar a fannoni da dama da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, kasuwanci, harkokin noma, gyra hanyoyi, da Kuma uwa Uba bangaren tsaro don wadannan abubuwa da gwamna Fintiri ya maida hankali a kansu abun godiya ga Allah ne.


Wugira yace idan aka dauki bangaren ilimi ya inganta bangaren ta Samar da kayakin karatu, da gyra makarantu harma da biyan kudin jarabawan kammala makarantar sakandaren wato WAEC da NECO. da dai sauransu.

Haka a bangaren kiwon lafiya ma ya gyara manyan asibitoci da dama a kananan hukumomi dake fadin jahar tare da Samar da magunguna da kayakin aiki na zamani harma da hadin gwiwar da wasu kasashen domin ganin inganta fannin kiwon lafiya dake fadin jahar baki Daya.


Haka Ka zalika a bangaren noma ya samarwa dubbain manoma takin zamani ingancaccen iri da Kuma tallafawa manoman musammanma wadanda ke yankunan karkara a wani mataki na bunkasa harkokin noma a jahar da zumar Samar da wadaceccen abinci.


Gwamna Fintiri ya samarwa matasa da ma mata aiyukanyi ta koyar musu da sana o I daban daban Wanda hakan yasa matasa dama mata sun samu sana ar dogaro da kansu.


Saboda haka nema Barista Sunday yake kira ga daukacin Al ummar jahar da sukasance masu yiwa gwamnati dama gwamnan adu ar domin Allah Ya bashi iKon cigaba da aiyukan Alheri da yakeyi a fadin jahar. Tare Kuma bashi hadin Kai da goyon baya a Koda yaushe.


Da yake magana dangane da cikan shekaru ashirin da biyar da Najeriya tayi a karkashin mulkin domokiradiya kuwa Barista Sunday nan ma yace an samu cigaba a wasu bangarorin wasu bangarorin Kuma an samu koma baya.


Yace ko dawowa kan turban domokiradiya da akayi bayan karewan Mulki soja wannan abun godiya ga Allah ne don ko ba komai an samu walwalan rayuwa.


Ya shawarci gwamnatin tarayya da tayi dukkanin abinda suka dace domin ganin an samarwa Al ummar saukin matsalar rayuwa da ake ciki a halin yanzu, ta fadada aiyukanta sosai a bangarorin noma koyarwa matasa da mata sana o I dogaro da kansu Wanda hakan zaitaimaka wajen rage radadin wahala da ake ciki.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.