Cikan Najeriya shekaru 25 akan turbar domokiradiya an bukaci gwamnati da ta bunkasa harkokin noma.





 A yayinda mulkin domokiradiya ya cika shekara a Shirin da biyar a Najeriya Al umma na cigaba da baiyana ra atoyinsu dangane da cigaba ko akasin haka a fadin Najeriya.


Alhaji Adamu Jingi Wanda akafi sani da Mai hange Kuma shugaban kamfanin NAFAN dake Jambutu a karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa, ya baiyana cewa ba shakka an samu cigaba a bangarori daban daban a yayinda aka samu akasin haka a wasu bangarorin.


Alhaji Adamu Jingi yece misalin a bangaren gine gine da hanyoyi an samu cigaba  saboda haka akwai bukatan gwamnatin tarayya ta Kara Kai mi wajen gudanar da aiyukan more rayuwar Al umma domin Samar da hadin Kai da ma wanzar da zaman lafiya mai daurewa.


Alhaji Adamu ya Kuma baiyana cewa a bangarori irin su ilimi, noma, kiwon lafiya an samu koma baya saboda haka nema ya ke kire ga gwamnatin tarayya da tayi dukkanin maiyiwa domin bunkasa harkokin noma Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen Samar da aikinyi a tsakanin Al umma musammanma milyoyin matasa zasu samu aiyukan dogaro da kansu.


Alhaji Jingi ya kamata gwamnatin ta Samar da kayakin aikin noman na zamani da ingancaccen iri da kayakin feshi Wanda hakan zai taimakawa manoman kwarin gwiwa fadda aiyukansu da zai basu damar wadata abinci a fadin Najeriya.


A bagaren ilimi da lafiya kuwa Alhaji Adamu ya shawarci gwamnati da ta maida hankali sosai tare da bada damar zuba jari a bangarorin domin bunkasa harkokin ilimi dama kiwon lafiya a tsakanin Jama a.


Ya Kuma shawarci Yan Najeriya da sukasance masu baiwa gwamnatin hadin Kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran magance kalubale dake ciwa gwamnatin kasar dama Al umma tuwo a kwarya da suka hada da tsaro, matsalar tattalin Arziki da dai sauransu.


Ya Kara da cewa kamata yayi Yan Najeriya karau ganiya wajen yin adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen tabbatuwar domokiradiya a Najeriya.


Tun a shekara ta 1999 ne dai Najeriyar ta koma kan turbar domokiradiya  Wanda Kuma tayi shuwagabanin kasa guda biyar a karkashin jam iyun PDP da APC.


Kawo Yan zu dai Najeriya tana da jihohi 36 hada da birnin tarayya Abuja da Kuma kananan hukumomi 774.


Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.