Jam iyar APC a jahar Gombe ta dakatar sakataren tsare tsaren jam iyar na jahar.
Shuwagabanin jam iyar APC a jahar Gombe sun dakatar da sakataren tsare tsare jam iyar APC a matakin jahar Sanusi Abdullahi bisa zarginsa da aikata laifuka ciki harda yiwa jam iyar zagon kasa.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa daga sakataren watsalabarain jam iyar na jahar Ambasado Moses Kyari ya fitar a Gombe
A cewar sanarwa bayan bincike da aka gudanar an same shi da kaifin yiwa jam iyar zagon kasa Wanda hakan yasa a mikawa kwamitin zantarwan jahar domin daukan matakin da ya dace.
Sanarwa ta Kuma baiyana cewa kwamitin zantarwan jahar ta dauki matakin haka ne bisa tsarin dokan jam iyar.
Comments
Post a Comment