Kungiyar red cross a jahar Taraba tabi sahun takwaririnta na gudanar da bikin ranan red cross ta duniya.

 





Daga Sani Yarima Jalingo.


Kungiyar agaji ta red cross a Najeriya shiyar jahar Taraba tabi sahun takwaririnta na duniya wajen gudanar da bikin ranan ta red cross na shekara ta 2024. Tare da Kiran gwamna Agbu Kefas da ya taimakawa kungiyar da kudade domin su samu damar gudanar da aiyukan agaji a fadin jahar.



Taken bikin na bana dai shine cigaba da taimakawa. An fara gangamin ne da tafiya akan hanya da mutane masu yawa a fadar jahar ta Taraba wato Jalingo.



Da yake jawabi shugaban red cross na kasa Oluyemisi Adega JP yace  sun bukaci kudi masu yawa daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kasancewa shine Uba a kungiyar ta red cross a Najeriya da sanata Oluremi Tinubu.




Shugaban kungiyar Wanda sakataren red cross a jahar Taraba Mr Manja Aggrey Martin ya wakilta yace shugaban yayi kira ga ofishin mataimakin shugaban kasa, da na shugaban majalisar dattawan, harda na kakakin majalisar wakilain, shugaban Alkalai na tarayya, ministoci dama dukkanin masu ruwa da tsaki da sukasance suna taimakawa kungiyar ta red cross.



Ya Kuma kirayi gwamnoni da Suma sukasance suna taimakawa ofishoshin kungiyar dake jihohi domin taimakawa Al ummah.



A nashi bangaren sakataren kungiyar ta red cross a jahar Taraba Mr Manja Aggrey Martin yace burinsu shine sukasance suna taimakawa Al ummah.



Mr Martin ya kirayi gwamnatin jahar Taraba karkashin shugaban gwamna Agbu Kefas da ma sauran masu ruwa da tsaki da su taimakawa kungiyar da motoci da zai basu damar gudanar da aiyukansu a fadin jahar.




Shima da yake nashi jawabi Aminu Umar Bashir  mashawarci a ofishin kungiyar a jahar Taraba ya yabawa wadanda ke taimakawa kungiyar ta red cross tare da Kiran su da su cigaba.



Mr A Yahuza ya yabawa Yan Sakai da suke taimakawa kungiyar tare da jinjina musu bisa kokari da sukeyi.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.