Kunguyar yan jarida na shiyoyin A E ta gudanar da taronta a jahar Gombe.
An yabawa shuwagabannin kungiyar Yan Jarida ta kasa NUJ dake shiyoyin A.E bisa na mijin kokari da sukeyi na gudanar da aiyukan cigaban kungiyar a shiyoyi dama kasa baki Daya.
Kungiyar tayi wannan yabane a takardan bayan taronta da ta gudanar a jahar Gombe. Dauke da sanya hanun mataimakin shugaban kungiyar na shiyar E da mataimakin shugaban kungiyar a shiyar A da sakataririnau da suka fitar Jin kadan da kammala taron.
Taron Wanda ya samu halartan shugaban kungiyar Yan Jarida mata NAWOJ dama shuwagabani da suka gabata, da wannan ne suke yabawa shuwagabanni musammanma Wanda ya gaiyaci taron Kuma shine mataimakin shugaban kungiyar ta kasa Mallam Alhassan Yahaya Abdullahi inda ya bada damar tattauna batutuwar cigaban kungiyar daban daban.
Kungiyar ta Kuma kirayi gwamnaonin jihohin dake shiyoyin da su gaggauta daukan matakin magance matsalar tsaro dake addabar yankunan da suka hada da Yan bindiga, Satan shanu,da dai sauransu domin samun cigaban jihohin
A taron kungiyar ta yabawa shuwagabanin hukumomin tsaro karkashin shugabancin Gen. Christopher Musa CDS bisa kokarinsu na inganta tsaro domin takawa Yan bindiga, masu garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa, dama aikata laifuka birki, a wani mataki na kare rayuka dama dukiyoyin Al ummah.
A lokacin taron an jajintawa Al ummar jahar Borno da gwamnatin jahar biyo bayan rasuwa Yan Sa Kai 9 da suka rasa ratuwansu a lokacinda suke bakin aiki. Tare da jajintawa kungiyar Yan Jarida na jahar Bauchi bisa rashin membanta Mallam Usman Tahir Wanda tsohon ma aikacin gidan TV Bauchine.
Dangane da hanyoyi kuwa kungiyar ta kirayi gwamnatin tarayya da ta dauki matakai da suka dace domin gyra manyan hanyoyin shiyoyin domin kawo karshen hatsura da ake samu akan hanyoyin baki Daya.
Harwayau kungiyar ta kirayi gwamnatoci a dukkanin matakai da su magance matsalar dalube da basa makaranta da Kuma kawo karahen matsalar yara da basa samun abinci maigina jiki a yankin Arewa masau yamma da arewa masau gabas.
Taron ya bukaci da gwamnatin tarayya ta umurci hukumar wutan lantarki ta kasa da hukumar dake rarraba wutanlantarki da su gaggauta dawo da wutanlantarki a wasu jihohi da suka hada da Gombe, Yobe, Adamawa, da Taraba Wanda suka samu matsalar wutan sakamokon barnatar da turakin wayoyin da akayi.
Biyo bayan matsalar karancin maifetur da ake fama daahi a kasa baki Daya kungiyar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin magance matsalar duba da yadda yanzu haka Yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali.
Taron ya kirayi gwamnaonin jihohin shiyoyin da su fadada aiyukansu ya Kai ga gyra kafafen yada labarai dama cibiyoyin kungiyar Yan Jarida dake jihohinsu.domin inganta aiyukan Yan Jarida yadda ya kamata.
A taron ya jinjinawa Yan Jarida dake shiyoyin biyu bisa jajircewarsu na aiyukan cigaba dama Gina kasa tare da Kiran su da sucigaba da haka.
An Kuma yaba da yadda ake samu kyakkawar halaka a tsakanin shiyar kungiyar na A da E an bukacesu da su Kara kaimi domin cigaban yankunan biyu
A yayinda kungiyar ke kokarin shirye shiryen taron na kasa nan gaba a wannan shekara an bukaci da sauran yankunan su bada dama yankin arewa su fitar da Wanda zai shugaban kungiyar ta kasa domin samun cigaba da nasara.
Mahalarta taron sun baiyana cewa Yan takaran da magoya bayansu su maida hankali wajen abinda zai kawo cigaban kungiyar dama kasa baki Daya.
Kwamitin da suka tsara takaradan bayan taron dai sun hada da Lynn Adda kwamitin amintattu na kasa a matsayin shugaban, sai Umar Sa Idu shugaban kungiyar Yan Jarida a jahar Bauchi memba, da Abba Murtala Sakataren kungiyar a jahar Kano memba.da Kuma Chiroma Ali Ibrahim Sakataren kungiyar a jahar Borno Shima memba.
Comments
Post a Comment