Majalisar masarautar Hamman Bachama ta mika ta aziyarta ga iyalen Marigayi Mallam Ibrahim Lamorde.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Hamman Bacham Homun Dr Daniel Shaga Ismaila a madadin majalisar sarakunan Bachama na mika ta azuyarsu ga iyalen tsohon shugaban hukumar EFCC Marigayi Ibrahim Lamurde.
Hamman Bacham yace ya Kadu kwarai da Jin labarin rasuwar Marigayi Ibrahim Lamurde tsohon shugaban hukumar EFCC.
Basaraken a wata sanarwa da ya fitar ya baiyana Marigayi Lamorde a matsayin jajircececcen mutu Kuma ya taka rawa wajen yaki da cin hanci da rashawa ya Kuma bada gudumawa sosai wajen aikin Dan sanda ya Kuma taka rawa wajen cigaban tattalin Arzikin Najeriya.
Baya ga iyalain Marigayi majalisar sarakunan Bachama na yiwa masarautar Mubi da gwamnati dama Al ummar jahar Adamawa ta aziyar rasuwar Marigayi Mallam Ibrahim Lamorde tare da Yi musa Adu ar Allah ya jikanshi yasa mutuwar hutuce.
In za a iya tunawa dai Mallam Ibrahim Lamorde ya zama shugaban hukumar EFCC a tsakanin shekara ta 2011-2015.
Comments
Post a Comment