Rashin ruwan Sama an bukaci da ayi adu ar rokon ruwa.

 




Majalisar Addinin musulunci a jahar Adamawa ta umurci rassarta dake kananan hukumomi ashirin da Daya dake fadin jahar da su maida hankali wajen shirya adu o I domin rokon Allah madaukakin sarki wajen samun ruwan Sama duba da yadda ake samun jinkiri ruwan Sama a jahar.


Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika ne ya bada wannan umurni a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da majalisar ta zantar da matsaya dangane da lamarin, a shelkwatar majalisar dake Yola.



Mallam Gambo Jika yace daukan matakin yin adu a ya zama wajibi duba da yadda ake cikin damina amman kawo yanzu a samun karancin ruwan Sama Wanda acewarsa ya kamata ace anyi nisa a harkokin damina Kuma har yanzu ba a Yi shukaba.


Saboda haka ya kamata Al umma musulmai su dukufa wajen yin adu o I domin rokon ruwa domin a samu ruwan Sama Wanda hakan zai baiwa manoma Samar gudanar da harkokinsu na noma yadda ya kamata.


Majalisar ta Kuma ja hankalin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dama masu ruwa da tsaki da su dauki matakin magance matsalar tsadar rayuwa da ake ciki a halin yanzu biyo bayan cire tallafin Mai ferur.


Malam Gambo Jika yace yanayi da ake ciki a halin yanzu komai yayi tsada Kuma lamarin sai cigaba yakeyi saboda haka ya kamata gwamnati ta dubi lamarin ta dauki matakin kawo karshen matsalar baki Daya.


Harwayau majalisar ta maida hankali a bangaren wutan lantarki nanma majalisar ta bukaci da kamfanin Samar da wutan lantarki a Najeriya da tayi dukkanin maiyiwa domin kawo karshen matsalar, domin a cewarsa sannu a hankali lamarin ya dauki tsawon lokaci ba tare da an dauki kwararan matakai a kaiba.


Mallam Gambo Jika ya kirayi Yan Najeriya sukasance masu cigaba da adu o I a Koda yaushe domin kawo karshen matsalar baki Daya 

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.