Rundunan yan sandan jahar Adamawa na cigaba da horar da Jami anta
A kokarinta na inganta aiyukan Jami anta yadda ya kamata rundunan yan sandan jahar Adamawa ta fadada horar da Jami anta har zuwa yankin Arewacin jahar ta Adamawa
An dai kammala horon ne a Mubi, rundunan yan sandan dai ta dauki matakin horar da Jami anta domin inganta aiyukansu domin samun cigaba.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace dalilin rundunan na daukan matakin horo ga Jami anta domin sun san yadda zasu san dabarun dakile aikata laifuka da Kuma gaggauta Kai dauki da zaran an samu labarin ana aikata ba daidaiba.
A jawabinsa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris Wanda mataimakinsa DCP Olubunmi Olubode Fakeye ya wakilta ya gabatar da mukalarsa akan dabaru da sanin yadda zasu gudanar da aiyukansu
Kwamishinan Yan sandan ya Kuma kirayi Al umma da sucigaba da taimakawa Yan sandan da wasu bayanai a kan lokaci da zai basu damar damke masu aikata laifuka.
Comments
Post a Comment