Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana cin nasaran yaki da masu aikata laifuka a fadin jahar.

 



A kokarinta na yaki da masu aikata laifuka dama watsar dasu daga maboyarsu daban daban da suka hada da Jimeta bypass, Jambutu, Yokkore, Tashan Tiopa, da Kuma kwalbatin Doubeli. Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta kama mutane 39 da ake zargi da aikata laifuka Wanda kawo yanzu ana cigaba da bincike kuma za a tabbatar da adalci a yayin bincike.


Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


Sanarwan ta Kuma shawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanain duk abinda basu amince da suba domin daukan matakin da ya dace Akai.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE