Rundunan yan sandan jahar Adamawa Tasha alwashin baiwa makarantu dake fadin jahar kariya.
A kokarinta na inganta tsaro a makarantu domin baiwa dalube kariya. Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta horar da Jami anta na musamman da zasu kasance masu sanya ido a dukkanin makarantu dake fadin jahar
Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace an horar da Yan sandan kwantar da tarzoma runduna na 14 dake nan Yola sanin dabaru daban daban domin Kai dauki da wuri. Kuma an gudanar da haka ne biyo bayan umurni da Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya bayar.
An dauki matakin haka ne saboda dakile aikata laifuka a makarantu a wani mataki na baiwa dalube dama malamain makarantu gwamnati Dana masu zaman kansu da dai sauransu.
Haka kazalika horarwa zaitaimaka wa rundunan wajen inganta tsaro a dukkanin makarantu dake fadin jahar.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris yace akwai bukatar Jami an su nuna kwarewarsu domin gudanar da aiyukansu yadda ya kamata ba tare da matsalaba.
Mataimakin kwamishinan Yan sandan jahar Olubode Olubunmi Fakeye shine shine zai jagoranci rundunan domin ganin an kare makarantu gwamnati da na masu zaman kansu.
Comments
Post a Comment