Wasu da ake zargi da aikin shila sun shiga hanun Yan sanda a jahar Adamawa.
Jami an yan sandan a jahar Adamawa sun kama wasu matasa biyar da suka addabi kasuwar Yola da angwanni wuro Hausa da Damare dukkaninsu a cikin Yola ta kudu, bisa zarginsu da kwace wayoyi da dai sauransu.
Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola
Sanarwan tace an ko yi sa a domin wadanda aka kama suna cikin jerin sunayen da suke nema ruwa a jallo.
Kawo yanzu dai ana cigaba da bincike domin tabbatar da doka tayi aiki akansu.
Rundunan yan sandan ta kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sucigaba da taimakawa rundunan da wasu bayanain sirri dama abunda basu yarda da lamarinsaba. Domin daukan matakin Akai.
Comments
Post a Comment