Wasu matasa biyu sun shiga komar Yan sanda bisa zarginsa da satar mashin Mai taya uku a jahar Adamawa.
A kokarinta na magance matsalar sace sace rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cika hanu da wasu matasa biyu da ake zargi da satar Keken NAPEP a lagin chochi a runde dake cikin karamar hukumar yola ta arewa.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace an samu nasaran kama wadanda ake zarginne bayan samun bayanain sirri da ofishin Yan sanda na yankin Jimeta ya samu Wanda hakan yasa na ayi da wasaba wajen Kai dauki Kuma akayi nasaran kama wadanda ake zargi.
Bincike ya nuna cewa kawo yanzu ba Akai ga kama ainihin Wanda ake zargi da Satan maahinba kamar wadanda suke hanun Yan sandan suka baiyana. Kuma an gono cewa mashin din mallakar wani Mai Suna Muhammed Sani ne.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya yaba da yadda ake bada bayanai akan lokaci tare da tabbatarwa Al umma cewa rundunan zataci gaba da Kai dauki akan lokaci matukan sun samu bayanai akan lokaci.
Comments
Post a Comment