Zuba Jari a harkokin P O S zaitaimaka wajen Samar da aikin yi a tsakanin matasan.

 




An shawarci gwamnati jahar Dana tarayya harma da masu hanu da shuni da sukasance suna masu maida hankali wajen zuba jari a harkokin POS domin samun cigaban tattalin Arziki da Samar da aikinyi musammanma a tsakanin matasa.


Alhaji Auwal Usman shugaban masu sana ar POS a jahar Adamawa ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da Jarida An nur Hausa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Alhaji Auwal yace zuba jari a harkokin POS Yana da matukan muhimmanci domin zaitallafawa rayuwar matasa harma da bangaren tattalin Arziki.



Usman yace kawo yanzu tan daga lokacinda aka fara wannan sana ar ta POS an samu cigaba domin an aka dubi yawan masu sana ar duk matasane saboda haka in har gwamnati da masu hanu da shuni zasu sanya hanun jari a cikin harkokin to ba karamin cigaba za a samu a.


Da wannan nema Alhaji Auwal yake shawartan matasan da aumaida hankali wajen koyon sana ar dogaro da Kai domin kare maryabansu da mutuncinsu a idon Al umma.


Acewarsa dai akwai sana o I da dama da matasan zasu iya koya da suka hada da tela, makanikaci, Gini, noma, da dai sauransu Wanda hakan zai kaisu Tudun na tsira.


A karshe ya kirayi Yan Najeriya da sukasance masu hada kansu da Kuma bada tasu gudumawar wajen Gina kasa da Samar da zaman lafiya tare dayin adu ar Neman taimakon Allah wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki Daya 

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE