An bukaci da masarautun gargajiya subaiwa hukumar NDLEA goyon baya.



Mai martaba Lamidon adamawa. Dr Barkindo Muhammadu Aliyu Mustafa ya kirayi masu rike da masarautun gargajiya da sukasance masu baiwa hukumar dake yaki da sarafa dashan miyagun kwayoyi NDLEA domin ganin an Samar nasara yakan Sha da sarafan miyagun kwayoyi a tsakanin Al umma baki Daya.


Maimartaba yayi wannan kirane a lokacinda tawagan hukumar ta NDLEA ta Kai masa ziyara a fadarsa dake Yola.


Lamidon Adamawa Dr Barkindo Muhammadu Aliyu Mustafa Wanda Dan Lawan Adamawa Alhaji Sadiq Umar Daware ya wakikilta ya baiyana cewa maimartaba ya nuna gamsuwarsa da yadda hukumar take gudanar da aiyukanta na yaki da hana Shan miyagun kwayoyi.


Alhaji Sadiq Umar Daware yace hakan yasa Mai martaba Lamidon Adamawa ya umurci dukkanin masu rike da masarautun gargajiya da su taimakawa hukumar a Koda yaushe domin ganin an Kai ga nasaran yakan matsaro.


Alhaji Sadiq ya Kuma kirayi Al umma musammanma iyaye dacewa suna suna da rawan da zasu iya takawa wajen yaki da hana Shan miyagun kwayoyi don haka su maida hankali wajen yaransu a Koda yaushe domin sanin halin da suke ciki.


Alhaji Sadiq ya Kuma shaidawa tawagan hukumar dacewa Mai martaba Lamidon Adamawa Yana gode musu Kuma a shirye yake ya basu hadin Kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu.


Ya Kuma shawarci matasa da su nisanta kansu daga duk abinda zai gusar musu da hankali domin sukasance jakadu na gari a tsakanin Al umma.


A jawabinsa kwamandan hukumar na shirya B Wanda ya kunshi jihohin Gombe, Taraba, da Adamawa Alhaji Bello Idris yace sun kasance a fadar maimartabanne domin Neman goyon bayansa dangane da yaki da hukumar takeyi da hanasha da fataucin miyagun kwayoyi.


Bello Idris yace hukumar tayi nasaran tsare tare da kama kayakin dasuke da halaka da kwayoyi da dama saboda haka nema suka shirya wannan gangamin a wani mataki na rananan yaki da miyagun kwayoyi ta duniya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.