An samu matsalaha a tsakanin kungiyar IPMAN da Kwastom biyo bayan da gwamnatin jahar ta shiga tsakani




 Shuwagabannin kungiyar dillalain maifetur masu zaman kansu IPMAN shiyar Jihohin Adamawa da Taraba tare da hukumar kwastom Najeriya NCS sun godewa gwamnatin jahar Adamawa bisa shiga tsakani da tayi domin sasanta tsakanin hukumar kwastom din da kungiyar ta IPMAN. Wanda hakan ya kawo karshen ta kaddama dake tsakaninsu.



Sakataren Kungiyar ta IPMAN a jahar Adamawa da Taraba Abdulmalik Bello Wanda shinema ya jagoranci tawagan kungiyar. Sai Kuma kwanturolan hukumar kwastom a jahar Adamawa Garba Bashir dukkaninsu sunyi alkawarin yin aiki tare domin Samar da cigaba.






Tunda farko a jawabinta mataimakiyar gwamna jahar Adamawa Farfesa Kaletapwa Farauta ta yabawa kungiyar ta IPMAN da hukumar kwastom bisa hakuri da sukayi da juna da fahintar juna a tsakaninsu.




Farfesa Farauta tace a madadin gwamnatin jahar Adamawa tana sanar da Al ummar jahar Adamawa cewa yanzu Kam ana sayar da maifetur a dukkanin gidajen maifetur dake fadin jahar.



Saboda haka tace an warware ta kaddama dake tsakanin bangarorin biyu Kuma an fahinci juna.saboda haka tana zaton kowa zai samu damar sayan Mai a gidajen Mai domin samun saukin rayuwa





Tace gwamnatin ta damu kwarai dangane da abinda ya faru saboda jama a suna cikin mawuyacin hali na matsalar tattalin Arziki.don haka bama bukatar wata matsala Kuma.



Saboda haka a madadin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa Muna Kara godiya ga IPMAN, Hukumar Kwastom, NATO, NNDPR dama dukkanin masu ruwa da tsaki dangane da batun.





Saboda  haka Muna godewa  kungiyar dama hukumar kwastom bisa saurarenmu da Kuma amsa Kiran gwamnati nayin duk abinda ya dace. domin warware matsalar.





Sakataren kungiyar ta IPMAN Bello yace Yana maishaidawa Al ummar jahar Adamawa cewa tunda gwamnatin jahar Adamawa ta shiga tsaka yanzu Kam an warware dukkanin batun baki Daya.




Don haka Muna Kiran dukkanin membobin kungiyar da su Bude dukkanin gidajen mainsu domin cigaba da sayarwa jama ar jahar Adamawa.



Da yake jawabi kwanturolan hukumar kwastom a jihohin Adamawa da Taraba Garba Bashir yace ya kira shelkwatar hukumar inda ya shaida musu halin da ake ciki Wanda hakan yasa suka bada umurnin yin sausauci domin baiwa Al ummar jahar damar gudanar da harkokinsu cikin tsanaki.



Yace nan gaba zasu wayarwa membobin kungiyar ta IPMAN Kai dangane da aiyukan hukumar domin kaucewa sake samun irin wannan matsalar 



Ya Kuma godewa gwamnatin jahar Adamawa dangane da Kiran wannan tattaunawa don samun matsalaha tare da godewa kungiyar ta IPMAN da NNDPR.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.