An taimakawa matan da mazajensu suka mutu da kudi domin bunkasa kasuwancinsu.
Daga Sani Yarima Jalingo.
Wata kungiyar maizaman kanta wato WAYOMTI dake jahar Taraba ta taikawa mutane shida da basu gurbin karatu harma da masuyin kaya.
An dai gudanar da bikin bada gurbin karatunne a dakin taro na Fwanya Plaza dake Jalingo fadar gwamnatin jahar.
Darectar kungiyar Mis Parisca Essene Joel tace an bada wannan taimakon Yana daga cikin manufar gungiyar domin tallafawa mata da maza ta wajen koya musu sana o I. Illimantar da su dama taimaka musu da abinda zaishafesu.
An dai zakulo wadanda suka amfana da Shirin ne ta hanyar tantancewa da musu tabbagoyi Wanda kwamitin amintattun kungiyar ya gabatar.
Mis Parisca Joel ya baiyana cewa cikin mutane shida da aka zaban an zabi mata uku maza uku daga cibiyar watsa labarain fasaha da dai sauransu.
Ta Kara da cewa an zabi mata da mazajensu suka mutu biyar wadanda aka taimaka musu da kudi domin su bunkasa harkokin kasuwancinsu.domin su dogara da kansu.
Kuma kungiyar tace zata sanya ido kan wadanda aka basu taimakon domin tabbatar da cewa Suna amfani da abinda aka basu ta yadda ya dace.
Darectar tayi alkawarin cewa kungiyar zata cigaba da horar da mutane sama o I irinsu yin takalma, Mai da dai sauransu sannan kungiyar zata fadada aiyukanta ta ciyar da marassa galihu Koda sau Daya a wata.
Don haka nema take kira ga mawadata dam kungiyoyi da sukasance suna taimakawa mabukata Tama shawarci gwamnatin jahar ta Taraba da ta hada Kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin samun nasaran gudanar da muradunta karkashin gwamna Agbu Kefas.
Wasu daga wadanda suka amfana wato Selina Danladi da Muhammed Sanusi Tukur sun baiyana Jin dadinsa da farin cikinsu dangane da wannan taimako da akayi musu Wanda Kuma irin wannan taimakon shine karon farko a rayuwarsu.
Itama anata bangaren Daya daga cikin matan da mazajensu suka mutu Kuma suka amfana da taimakon Usaina Dankano ta baiyana farin cikinta dangane da wannan taimako da akayi musu Wanda zai taimaka musu a harkokin kasuwancinsu ma tsawon lokaci.
Comments
Post a Comment