Gwamnatin jahar Taraba Tasha alwashin bunkasa harkokin wasanni a fadin jahar.






Daga Sani Yarima Jalingo.


 Gwamnan Agbu Kefas na jahar Taraba yace gwamnatinsa zata cigaba da bunkasa harkokin wasanni ta ma aikatan wasanni da matasa domin cigaban wasanni a fadin jahar.




Gwamnan Wanda shugaban ma aikatan gwamnatin jahar Paul Tino ya wakikta shi ya baiyana haka a lokacin bikin kaddamar da wasan Olympic Wanda ya wakana a dandalin wasa na Jolly Nyame dake Jalingo.





Yace taron ya Nuna cewa  jahar batayi da wasaba wajen inganta aiyukan wasanni don haka nema yace ta irin wannan taron ne matasa zasu samu basira gudanar da harkokin wasanni.



Ya Kara da cewa a yadda aka Sani wasa Yana hada zumunci da hada Kai a tsakanin Al ummah Wanda hakan yakan Kai ga nasaran samun cigaba.





Gwamnan ya Kuma yabawa ma aikatar matasa da  wasanni jahar karkashin shugabancin Joseph Joshuwa bisa gudanar da aiyukan bunkasa harkokin wasanni. Wanda Kuma hakan yana cikin kuduroein gwamnati biyar.




Yace a yadda ake gudanar da wasan Olympic jahar ta irin nasarori da cigaba da aka samu a cikin shekara Daya.





Shugaban kwamitin wasan Olympic ta kasa Injiniya Habu Gumel Wanda Mr Jesse Galadima ya wakilta yace wannan rana da aka kirkiro domin gudanar da wasan na Olympic ranane Wanda Pierre de Coubertin ya kirkiro.




Gumel Wanda Kuma shinema ya wakilci shugaban kwamitin Olympic din ta kasa da kasa Thomas  Bach ya baiyana wasan a wannan shekara a matsayin ma musammanne duk dacewa wasan Wanda za ayi a Paris na shekara ta 2024 na daf da zuwa.





Tunda farko a jawabinsa na maraba kwamishina matasa da wasanni a jahar Taraba Joseph Joshua yace bikin ba wai da wasanni kawaiba harma da kiwon lafiya da Kuma hadinkai.




A tattaunawarsa da manema labarai shugaban kwamitin harkokin wasanni a majalisar dokokin jahar Taraba Kuma memba Mai wakilta Karim Lamido Anas Shu aibu ya baiyana bikin a matsayin irin aiyukan cigaba da gwamna Kefas yakeyi harma da samarwa matasa aikinyi.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE