Gwamnatin tarayya Tasha alwashin kawo karshen matsalar tsaro.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta lashi takwabin takawa Yan bindiga birki a fadin Najeriya musammanma yankin arewa masau yammacin Najeriya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya baiyana haka a lokacin da yake jawabi a wurin taro kan tsaro da aka gudanar a jahar Katsina.
Shugaba Tinubu Wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta yace gwamnati zatayi dukkanin abinda suka dace domin ganin an dakile aiyukan Yan bindiga a fadin Najeriya.
Kashim Shettima yace Yana da muhimmanci a samu kakkawar halaka da hadin Kai a tsakanin hukumomin tsaro dama Al umma domin hakan zaitaimaka kwarai wajen dakile aiyukan masu tada kayan baya.
Ya Kuma kirayi Yan Najeriya da su cigaba dayin adu o I a Koda yaushe domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen matsalar tsaro.
Itama a nata bangaren ministar Matasa da wasanni a Najeriya Dr Jamila Bio Ibrahim tace zasu maida hankali wajen koyawa matasa sana o I dogaro da Kai Wanda a cewarta hakan zaitaimaka wajen rage radadin ta addancin.
Ta shawarci matasan da sukasance masu Neman sana ar dogaro da kai domin Suma su bada tasu gudumawar wajen cigaban kasa dama wanzar da zaman lafiya.
Comments
Post a Comment