Kungiyar IPMAN a jihohin Adamawa da Taranba ta rufe dukkanin gidajen maintain a jahar Adamawa.
Kungiyar dillalain Main ferur da dangoginsa masu zaman kansu a Najeriya IPMAN shiyar jihohin Adamawa da Taraba, ta sha alwashin cigaba da rufe gidajen Mai dinsu sai in fa hukumar hana fasa kwabri ta sake musu wato kwastom ta sake musu motocinsu da ta kama.
Shugaban kungiyar ta IPMAN a jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Dahiru Buba ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Alhaji Dahiru Buba yace kungiyarsu baza ta lamunci abunda hukumar kwastomdin take Yi musuba. Wanda acewarsa sun ba yadda za ayi su sayi Mai da tsada Kuma Azo ana kama musu mai ba saboda su ba Yan fasa kwabri bane.
Alhaji Dahiru Buba yace sun dauki matakine rufe gidajen maidinsune saboda nuna fushinsu da rashin jindadinsu dangane da abinda hukumar kwastom din ke musu, domin abune da bai kamata ace hukumar tayi musu haka ba.
Dahiru Buba ya baiyana cewa operation Whirld wing karkashin hukumar kwastom din a matakin tarayya ne suke kama musu motoci da sunan suna fasa kwabri Wanda Kuma suna kasuwancinsune ba fasa kwabri sukeyiba.
Dahiru Buba yace sai dai in gwamnati zata sayi Mai fetur din ta ta rarraba badamuwa to amman sukam bazasu Bude gidajen maisuba har sai an daina kama musu motocinsu da rufe musu gidajen Mai.
Alhaji Dahiru Buba ya Kuma tabbatarwa Al umma cewa su Sani wannan matsalar ba daga wurinsu bane Kuma da zaran sun warware matsalar dake tsakaninsu da hukumar kwastom din zasu Bude gidajen mainsu.
A cewarsa dai ba yadda za ayi mutum ya cire kudinsa har Sama da Milyon talatin ya sayi Mai amman a rinka kama musu motoci ko a rufe musu gidajen Mai wannan na daidai bane,
Harwayau yace suna cigaba da tattaunawa domin kawo karshen wannan ta kaddama da ke tsakanin hukumar kwastom da kungiyar tasu ta IPMAN.
Rufe gidajen Mai din dai yayi sanadiyar ta kaita zirga zirgan ababen hawa da Kuma tsadar kayakin masa rufi da dai sauransu a ciki da wajen gwamnatin jahar Adamawa..
Comments
Post a Comment