Kungiyar IPMAN ta janye yajin aikin da ta shiga a jahar Adamawa.

 




Kungiyar dillalain Mai fetur da gamgiginsa masu zaman kansu a Najeriya IPMAN na shiyar jihohin Adamawa da Taraba ta dakatar da yajin aikin da ta shiga biyo bayan wata tankiya da ta shiga tsakaninsu da hukumar kwastom.


Shugaban Kungiyar a jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Dahiru Buba ya shaidawa Jaridar An NuR Hausa cewa biyo bayan shiga tsanmkani da gwamnatin jahar Adamawa tayi, hakan yasa aka warware matsalar.


Alhaji Dahiru Buba yace kawo yanzu komai ya koma dai dai saboda sun janye yajin aiki, Kuma zasucigaba da gudanar da aiyukansu kamar yadda suka saba, ba tare da wata matsalaba.






Alhaji Dahiru yace hukumar ta kwastom zata mika motocin maisu da takama ga hukumar dake kula da dai dai ta farashin Mai domin tabbatar da ingancin Mai din sai a mika musu kayansu domin su sayar da shi.


Saboda haka sun warware kowane matsalar a tsakaninsu, ya Kuma tabbatar da cewa zasu cigaba da aiki da hukumomin tsaro dama kwastom din tare dama mutunta juna a Koda yaushe domin samun hadin Kai a tsakaninsu.





Yajin aikin da kungiyar ta IPMAN ta shiga dai ya tsakaita zirga zirgan ababen hawa na karamin lokaci Wanda ya haifar da hawhawar farashin sifiri dama kayakin masarufi.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.