Kungiyar malamai Jami o I a Najeriya ta bukaci da gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniya da suka cimma atsakaninsu.
Kungiyar malamain Jami o I a Najeriya ASUU shiyar Jami ar Modibbo Adama dake Yola, ta bukaci da gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniya da suka cimma a tsakaninsu.
Shugaban kungiyar a shiyar Jami ar Modibbo Adama dake Yola. Dr El Moude Jibrin Gambo ne ya baiyana haka a lokacinda yake yiwa manema labarai jawabi a harabar Jami ar da Yola.
Dr El Moude Jibrin yace yiwa manema labarai ya zama wajibi saboda su fadakar da mutane irin Takun Saka dake tsakanin kungiyar ta ASUU da gwamnatin tarayya saboda akwai rashin fahintar a tsakaninsu lamarin da yake ciwa kungiyar tuwo a kwarya na tsawon shekaru.
Dr El Maude Gambo yace akwai mutane da dama da suke zargin kungiyar ba tare da sun fahinci damiwar kungiyar ba saboda haka akwai bukatan mutane su fahinci irin gwagwarmaya da kungiyar keyi saboda a hada Kai aiyi aiki tare domin ceto bangaren ilimin dake fadin kasan nan.
Dr Jibrin ya baiyana cewa akwai batun watanni takwas da sukayi yajin aiki a shekara ta 2022 da Kuma yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin a shekara ta 2019 Wanda kawo yanzu gwamnati bata magancesiban. Saboda haka su basu bukatar sabon Abu abinda sukeso shine gwamnatin ta aiwatar da yar jejeniya da sukayi a shekaru da suka hada da na 2017,2018,2019,2020,da 2022.wadanda suka hada da inganta Jami o I gwamnati , da kudin Alawus Alawudin malamai, da batun Jami o I jihohi, da dai sauransu.
Dr Gambo yace abin takacinma shine gwamnati tayi biris da lamarin Wanda Kuma hakan ya sanya dalube rashin tabbas a bagaren ilimi Wanda yanzu haka ana tsakiyar shekara ta 2024.
Dr Gambo yace kungiyar tasha zama da wakilain gwamnatin tarayya na tsawon lokaci amman har yanzu ba a cimma gaciba.
Harwayau Dr Jibrin ya ja hankalin gwamnatin tarayya da tayi dukkanin maiyiwa domin aiwatar dama cika alkawura da ta dauka domin ganin an samu cigaba Jami o in dama ilimi a fadin kasar baki Daya.
Comments
Post a Comment