Matsalar tattalin Arziki an bukaci gwamnati da ta taimakawa Yan kasuwa da manoma.

 





An kirayi Yan kasuwa dake fadin Najeriya da sukasance masu sanya tsaron Allah madaukakin sarki a harkokin kasuwancinsu domin samun sauki rayuwa dama rage wahalar rayuwa dake ciki a halin da ake ciki a yanzu.


Shugaban kungiyar Yan kasuwar Arewacin Najeriya Kuma Galadiman Yola Alhaji Muhammed AbdulKadir Ibrahim ne ya baiyana haka a zantawarsa da Jaridar An NuR Hausa dangane da yanayin matsalar rayuwa da ake fuskanta.




Alhaji Muhammed Ibrahim 86 yace ya kamata Yan kasuwa sukasance masuyin sausauci a kasuwancinsu domin taimakawa marassa galihu a wani mataki na samun albarkan kasuwancinsu.


Alhaji Ibrahim ya shaidawa Al umma cewa wannan lamari na hawhawar farashin kayaki Yana faruwa  ne sakamokon karayar tattalin Arziki da yadda maifetur da gasa ya Kara kudi biyo bayan cire tallafin Mai fetur da gwamnatin tarayya tayi.




Alhaji  Ibrahim ya Kuma kara da cewa mutane su sanifa wannan tsadar kayakin yan kasuwanma ba dadin lamarin suke jiba domin hakan yayi sanadiyar karyewar wasu saboda yadda irin matsanancin tattalin Arziki da ake ciki.


Alhaji Ibrahim AbdulKadir ya shawarci yan kasuwan da sukasance masu rage farashin kayakinsu su kaucewa cin riba maiyawa sunema albarkan kasuwancinsu.


Harwayau Alhaji Ibrahim ya kirayi gwamnatin tarayya da ta kasance tana sanya idon akan kamfanoni da Kuma rage musu kudaden haraji domin a cewarsa hakan zaitaimaka wajen samarwa Al umma saukin rayuwa.





Ya Kara da cewa ya zama wajibi gwamnati ta shiga domin itace take da wuka da nama ta Kara kaimi wajen maida hankalin akan kamfanoni domin samarwa Al umma sauki.


Da wannan nema yake kira ga gwamnatin tarayya Dana jihohi da su maida hankali wajen taimakawa manoma musammanma kananan manoma da kayakin noma na zamani domin a cewarsa rashin tallafawa manoma Yana Daya daga cikin halin da muka tsinci kammu a ciki.


A cewarsa dolene gwamnatoci a dukkanin matakai su tashi tsaye wajen bunkasa harkokin noma ta hanyar kayakin zamani domin a halin yanzu manoma na fuskantar matsaloli sosai saboda rashin wadadattu kayakin aiki musammanma ma zamani.


Don haka dolene a koma noma saboda a samu wadaceccen kayakin abinci domin gashi kayan miyama Yana kokari ya gagari mutane saboda rashin baiwa noma muhimmanci, saboda haka wannan kalubalene ga gwamnatoci su maida himma wajen agazawa manoma.



A cewarsa dai noma Yana da mutukan muhimmanci baya ga Samar da abinci Yana Samar da aikinyi a tsakanin  matasa ga Kuma inganta tattalin Arziki.


Alhaji Ibrahim 86 ya sahawarci yan Najeriya da sukasance suna baiwa shuwagabani hadin Kai da goyon baya da Kuma Yi musu adu o I domin ganin sun samu nasaran gudanar da aiyukan inganta rayuwar Al umma.


Haka Kuma ya ja hankalin Al umma su baiwa sarakunan gargaji hadin Kai kasancewa sune iyayen kasa Wanda hakan zaitaimaka wane samun cigaban zaman lafiya.



Ya shawarci yan Najeriya da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe da Kuma cigaban da adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro dake ciwa gwamnatocin kasan nan tuwo a kwarya..

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.