Matsalar tsaro an gudanar da taro kan matsalar tsaro kan yankin arewa masu yamma a jahar Katsina.

 




Biyo bayan matsalar tsaro da yankin arewa masau yamma ke fuskanta an gudanar da taron masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro a jahar Katsina dake arewa masau yammacin Najeriya.



Kakakin rundunan yan sandan Najeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Abuja.




Taron Wanda ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, Babban sifeton Yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun, da masarautun gargajiya Jami an sojoji, shuwagabannin Al umma  masana harkokin tsaro duk sun halarci taron da zumar tattaunawa domin samo matsalaha da zaman lafiya a yankin.




Harwayau taron ya samu halartan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sarkin Sokoto, Babban directan hukumar tattara bayanain sirri ta kasa NIA, da ma tsohon gwamnan jahar Katsina Bello Masari.



A sakonsa da ya gabatar a wurin taron Babban sifeton Yan sandan Kayode Egbetokun ya baiyana irin kokari da rundunan Yan sandan keyi na maido da doka da oda a yankin da Kuma yadda rundunan ke yaki da masu tada kayan baya, tare da cewa rundunan tana gudanar da aiyukanta ne bisa kwarewa da Kuma dabaru daban daban.



Babban sifeton Yan sandanya baiyana irin muhimmanci da Al ummah dake taimakawa Yan sandan ke dashi Wanda hakan ya taimaka kwarai wajen hadin Kai da goyon baya da aka samu a tsakanin Yan sandan da Al umma a hakan ya inganta tsaro yadda ya kamata.




Dafatan taron da aka gudanar zai zama silan Samar da hanyoyin da ma samun nasaran yakan Yan bindiga musammanma da yadda ake gudanar da farmaki daga rundunan operation Puff Adder, Operation Hadarin Daji, da dai sauransu Wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro  dama tarwatsa Yan bindiga, masu garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa a yankin.



Duk da wannan nasarori da aka samu Babban sifeton Yan sandan yace akwai sauran Rina a kaba saboda akwai bukatar Samar da dabaru da kuma samun hadin Kai a tsakanin Al umma da hukumomin tsaro dama kare hakkin bil Adama domin Samar da wadaceccen tsaro a yankin.





A jawabinsa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bada shawaran cewa a Kara samu Al umma da zasu kasance masu taimakawa hukumomin tsaro Wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen cigaban tsaro.



Ya Kuma baiyana cewa akwai bukatar samun kyakkawar halaka da hadin Kai a tsakanin hukumomin tsaro dayin aiki tare domin magance matsalar baki Daya.



Ya Kuma tabbatarwa Yan Najeriya cewa za a inganta harkokin tsaro a fadin Najeriya ,musammanma yankin arewa masau yamma domin in har Najeriya ta Gaza a harkokin tsaro to Afirka ma ta Gaza.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE