Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tana aniyar Samar da sashin da zai dakile aikata kunan bakin wake..
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta kudiri aniyar Samar da wani sashin da zai sanya ido kan yadda wasu ke jefa kansu cikin hatsarin kunan bakin wake.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola.
Sanarwan tace an dauki matakin haka ne duba da yanayi da ake ciki Wanda hakan kan sanya matasa yin kunan bakin wake, don hakane rundunan taga ya kamata a dauki matakin kare matsalar.
Sanarwan ta Kara da cewa matakin zai taimaka wajen canjawa matasan tunanin domin su kaucewa shiga hatsarin yin kunan bakin wake.
Runduna yan sandan ta nemi hadin Kai dama goyon bayan masu ruwa da tsaki dangane da matsalar domin ganin ta cimma burinsa na kawo karshen matsalar da ke sanya matasan aikata kiman bakin wake.
Comments
Post a Comment