Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tace a kimtse take ta baiwa manoma kariya.
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin baiwa manoma dake fadin jahar kariya a yayinda da suke gudanar da aiyukansu a gonakainsu domin Samar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya a wani mataki na bunkasa harkokin noma a fadin jahar.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya Samar da haka a zantawarsa da manema labarai a birnin Yola.
Kakakin yace duba da yanayi da ake ciki na matsalar tsaro rundunan yan sandan ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a samu wata matsalaba a tsakanin manoma da makiyaya.
Ya shawarci manoma da suke g9nakansu su gudanar da harkokin su cikin tsanaki domin rundunan ta shirya wajen inganta tsaro a dukkanin ganakai dake ke fadin jahar domin baiwa manoman damar yin noma ba tare da tsangwamaba.
SP Suleiman Yahaya yace jahar Adamawa an samu kauciyar hankali musammanma a tsakanin manoma da makiyaya saboda makiyayi da manomi Dan Jumma ne da Dan Jummai Kuma dukkansu suna noma saboda haka bai kamata ace ana samu ta kaddama a tsakaninsuba.
SP Nguroje ya Kara da cewa Yana daga cikin matakai da suka dauka na kada kwamitin wadanda suka da wakilain makiyaya da na manoma da sarakunan gargajiya Wanda acewarsa hakan ya taimaka matuka wajen dakile matsalar.
Ya Kuma kirayi manoma da makiyaya da su kaucewa daukan doka a hanu indan har sunga abinda bai kamataba to su gaggauta Kai rahoton ga hukumomin tsaro domin daukan matakin a Kai.
Rikici a tsakanin manoma da makiyaya dai ya dade Yana ciwa gwamnati tuwo a kwarya lamarin da ke janyo asarar rayuka dama dukiyoyi masu yawa.
Comments
Post a Comment