Wani da ake zargin da harbe mutane biyu jarlahira ya shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa.
Jami an Yan sanda a jahar Adamawa sun kama wani danbanga Mai Suna Mali Emmanuel maishekaru 31 bisa zarginsa da kashe Emmanuel Hamma Shehu da Almod Hamma Shehu dukkaninsu mazauna kauyen Bori dake cikin karamar hukumar Jada. a jahar Adamawa.
Jami I Mai hulda da jama a na rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a Yola.
Wanda ake zargin dai sun Sami sabani ne da wadanda ya hallakan ne a akan gona Wanda hakan yasa yayi amfani da adakan dake hanunsa ya harbi margayan Wanda Kuma hakan yayi sanadiyar mutuwar su.
Sanarwan ta baiyana cewa an cigaba da bincike dangane da lamarin.
Comments
Post a Comment