An baiyana muhimmanci taimakawa marayu abune ya yake da mutukan muhimmanci

 




An shawarci daukacin Al umma musulmai da sukasance masu tallafawa marayu a bangarori daban daban domin inganta rayuwarsu da Kuma samun kada Mai yawa ranan gobe kiyama.



Shugaban gidauniyar AYTAM a jahar Adamawa. Hakimin Hong Dan malikin Adamawa Alhaji Umar Babangida Mahmud ne ya bada wannan shawara a lokacinda yake jawabi a wurin bikin rufe musabkan karatun Al kur ani, Wanda gidauniyar AYTAM ta ahiry wa marayu zalla Wanda aka gudanar a makarantar Al Huda dake Bachure dake Yola.




Alhaji Umar Babangida yace tallafawa marayu Yana da mutukan muhimmanci a rayuwa Al umma musulmai kamar yadda manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace duk Mai yiwa maraya hidima zai zama makwabcinsa a Aljanna. Saboda haka wannan damace ga Al umma musulmai.




Ya Kuma ja hankalin marayun da su maida hankali su wajen Neman ilimin addini da na zaman domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya kamata.



Har wayau ya kirayi matasa da kada su tsoma kansu wajen shiga zanga zanga da ake da aniyar a fadin Najeriya domin a cewars duk Wanda yace aiyi zanga zanga to bai Santa bane. Saboda haka zanga zanga ba zai kawo cigaba ba.



A cewarsa ya kamata Al umma su Sani komawa ga Allah madaukakin sarki tare da yin adu o I itace mafita ba wai ayi zanga zangaba don haka Al umma su guji tayar da fitina a tsakanin Jama a.



Alhaji Gambo Jika shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Wanda Kuma shine shugaban taron ya baiyana Jin dadinsa dangane da shirya wannan gasar ga marayu zalla tare da tabbatar da cewa a shirye yake ya kasance Yana baiwa gidauniyar hadin da goyon baya a Koda da yaushe.



Ya Kuma taya wadanda suka ahigasar murna musammanma wadanda sukayi nasaran tare da ahawartansu da sucigaba da karantun Al Qur ani  Mai girma a Koda yaushe domin inganta karatumsu.



Shima yayi gargadi ha matasa da kada a yaudaresu da shiga zanga zanga da bata da amfani saboda haka sukasance masu karatun ta nitsu kar su yarda ayi amfani da su wajen tarwatsa kasa ko lalata dukiyoyin Al umma.



Da yake nashi jawabi kakakin majalisar dokokin jahar Adamawa Bathia Wesley Wanda Kuma shine Babban Bako a wurin bikin ya tabbatar da goyon bayansa ga gidauniyar ta AYTAM a Koda yaushe Kuma a shirye yake ya cigaba da taimakawa gidauniyar yadda ya kamata.



A karshe Shima ya shawarci matasa sukasance masu bada gudumawa wajen cigaban kasa ba wai su zama masu wargasa kasaba saboda haka su nisanta kansu da shiga zanga zanga Kuma sukasance masu bin doka da oda a Koda yaushe domin Samar da zaman lafiya dama cigaban kasa.



Amisa itace ta kasance gwarzuwa a yayinda Bello ya kasance gwarzo a gasar Suma wadanda suka samu nasara a sauran rukunonin sun samu kautuka daban daban.


Akalla dalube marayu dari uku ne wadanda suka fito daga kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar Adamawa ne suka shiga gasar ta bana wato shekara ta 2024.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE