An bukaci da Al umma musulmai sukasance masu surka karatun yaransu Dana addini da na zamani.






 An tunatar da Al umma musulmai da sukasance masu Neman ilimin addini Dana zamani domin samu cigaban addinin musulunci.



Ustaz Muhammed Sani Umar Bako mamallakin makaratan Aljadid Jimeta ne yayi wannan tunatarwan a lokacin da yake jawabi a wurin bikin bada kaututtuka wamda makarantar Al Huda dake Bachure ta shirya a karamar hukumar yola ta Arewa.




Ya shawarci malamai da sukasance suna baiwa daluben ingancaccen ilimi Wanda hakan zai taimaka wajen samun ingancaccen tarbiya dama halaye na gari domin cigaban Al umma.




Da yake nashi jawabi baki Mai jawabi Dr Jabir Abdullahi ya yabawa Wanda ya Samar da makarantar bisa kokarinsa na inganta ilimi musammanma da ya hada dana addini harma Dana zamani.




Dr Abdullahi ya Kuma kirayi iyaye da Suma su taimaka wajen sanya ido akan yaran domin ganin sun samu ilimi Mai nagarta, harma yace baiwa yaro ilimin addini Yana da mutukan muhimmanci domin kuwa zai samu tarbiya nagari da zai zama abin koyi.




Shima nashi bangaren Dr  Aliyu Abdullahi Basullube ya koka da yadda wasu Al umma musulmai musamman iyaye basa baiwa ilimin addinin muhimmanci. Inda yace illimin addinin Kuma shine zaitaimaka a ranan gobe kiyama. Saboda haka akwai bukatar maida hankalin wajen karantar illimin addinin musulunci.




Dr Basullube ya kirayi Al umma musulmai da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa tsaron Allah da gaskiya Wanda hakan zai Kai su ga shiga Aljanna.




Da yake nashi jawabi mamallakin makaratar Al Huda dake Bachure cikin karamar hukumar yola ta arewa yace an kirkiro makarantar ne tun a shekara ta 2011. Kuma an farane da dalube 20 Wanda Kuma a yanzu haka makarantar tana da dalube kasi hamsin.




Yace manufar makarantar dai itace baiwa yara ilimi da Kuma basu kyakkawar tarbiya domin Suma su bada tasu gudumawa wajen cigaban kasa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.