An bukaci shuwagabanin kananan hukumomin da su maida hankali wajen yiwa Al umma aiyukan cigaba.

 




Mashawarci na musamman kan harkokin jama a ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri Barista Sunday Wugira ya taya shuwagabanin kananan hukumomi da aKa zaba Kuma aka rantsar da su murna samun nasara da sukayi  tare da Kiran su da sugudanar da aiyukansu bilhakki da gaskiya domin samun cigaban kananan hukumomi dake jahar Adamawa.


Barista Sunday Wugira ya baiyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Barista Sunday yace an rantsar da ahuwagaban kananan hukumomin akan gaba saboda yadda zasu samu kudade da zasu gudanar da aiyukansu biyo bayan hukumcin kotun koli da ya yanke ma bashi gashin kansu, saboda haka wannan damace agaresu da su maida hankali wajen yiwa Al ummarsu aiyukan cigaba.


Barista Wugira ya ja hankali Jama a da su kaucewa zuwa gun shuwagabanin da sunan Neman abinda za a basu susa a Aljuhu maimakon haka ya kamata su Kai musu kukan abinda yake ci musu tuwo a kwarya da suka shafi matsalar magudanain ruwa da dai sauransu.



Da wannan nema yake shawartan Al umma da sukasance masu tsafcace muhallimau a Koda yaushe da daina zuba shara a magudanain ruwa domin kaucewa ambaliyar ruwa.



Barista ya kirayi matasa da Suma sukasance masu Neman sana o In dagaro da Kai a Koda yaushe domin kare martabarsu a idon Al umma, Wanda hakan zaitaimaka musu wajen bada tasu gudumawa wajen cigaban tattalin Arziki a jahar dama kasa baki Daya.



Ya Kuma jinjinawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa jajircewa da Yayi na sakewa shuwagabanin mara domin su gudanar da aiyukan cigaban Al ummarsu yadda ya kamata.



Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE