An fara masabakar karatun Al Qur ani ga marayu zalla a jahar Adamawa

 




An Bude gasar Karatun Al Qur ani ga marayu zalla Wanda ake a duk shekara karkashin gidauniyar AYTAM a jahar Adamawa.


An dai Bude gasar ne a makarantar Al Huda dake Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.


Da yake jawabi a wurin bikin shugaban AYTAM a jahar Adamawa, Hakimin Hong Kuma Dan malikin Adamawa Alhaji Umar Babangida Mahmud ya nuna godiyarsa ga Allah madaukakin sarki tare da baiyana cewa wannan gasar da za a gudanar na marayu ne kadai saboda haka Yana Mai fatan za a gudanar da ahi bisa tsari.



Ya Kuma tabbatar da cewa za a gudanar da gasar da ba a taba yin irinsa ba da yaradana Allah a jahar Adamawa inda yace za ayi adalci ga dukkanin dalube da suka shiga gasar.



Don haka ne ma ya kirayi Al kalai da suyi adalci a lokacinda suke tantance wadanda sukayi nasara. domin ganin kowa anbashi abunda ya samu.


Daga nan sai shugaban wato Alhaji Umar Babangida Mahmud ya bada umurnin Bude gasar a ranan 26-7-2024. 


Shima a jawabinsa Ko odinaton gasar Mallam Garba Ahmed yace wannan Karo na biyu kenan ake gudanar da irin wannan gasar a jahar Adamawa.


Ya Kuma karancin dukkanin wadanda suka halarci bikin Bude gasar harma da daukacin dalube da suka zo daga sassa daban daban dake jahar Adamawa.


Dalube da dama ne dai wadanda suka fito daga daukacin kanana hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa ne dai suka shiga gasar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE