An yaba da aiyukan da gwamnatin Fintiri da takeyi na cigaban al ummar jahar Adamawa.
Mazauna unguwar Dundore dake cikin karamar hukumar Yola ta kudu a jahar Adamawa sun kirayi gwamnatin jahar da yayi musu adalci dangane da abinda hukumar wutan lantarki wato TCN tayi musu ma sanya musu Jan fainti a gidajensu da sunan za a kafar turakun wutan lantarki.
Shugaban kwamitin Al umma unguwar Alhaji Muhammed Gwani ne ya yi wannan kira a lokacin da sukayi gangamin nuna damuwarsa da faruwan wannan lamari domin acewarsa lamarin bai musu dadiba.
Alhaji Muhammed Gwani yace gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na taka rawan gani wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar dama Al ummar jahar Kuma gwamnati ce Mai Jin tausayin jama a don haka suna bukatar gwamnati ta shiga tsakani domin share musu hawayensu.
Muhammed Gwani yace a iya wayomsa Sama da shekaru arba in da biyar baya ba wata gwamnatin da yakeyiwa talakawa aiki face gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri don haka suna da yakinin gwamna Fintiri za share musu hawayensu.
Alhaji Gwani ya Kuma baiyana cewa sukam bazasu hana aikiba amman abinda sukeso shine a biyasu diyyan gidajensu domin a cewarsu in an fiddasu daga gidajensu Ina zasuje Kuma gashi wa adin mako biyu kacal aka basu.
Saboda haka suna rokon gwamnati Mai adalci ta dubesu da idon rahama domin kada rayuwarsu ta fada cikin wani yanayi na matsalar rayuwa.
Shima a jawabinsa Mallam Muhammed Isa Wanda shinema Mai unguwar na Dundore ya shawarci gwamnati da ta taimaka ta shiga tsakani saboda a biya jama a da lamarin ya shafa domin su samu sukuni da su da iyalensu.
Malam Muhammed Isa yace gwamnati itace uwa Uba saboda haka yake Kai kikansa ga gwamnati domin ita maijin kake koken Jama a ne. Kuma Yana fatan gwamnatin zataji kikansu domin ta magance musu matsalar.
Ya Kuma kirayi Al ummar unguwar ta Dundore da su daina Jin jita jita sukasance masu hada kansu domin samun cigaban unguwar dama zaman lafiya baki Daya.
Comments
Post a Comment