Gidauniyar AYTAM: An rantsar fa kwamitocin. da zasu gudanar da musabakar karatun Al Qur ani ga marayun a jahar Adamawa.
A yayinda ya rage kwanaki kadan a gudanar da gasar Karatun Al Qur ani Mai girma ga marayu zalla, a jahar Adamawa. Hakimin Hong Umar Babangida Mahmud ya kaddamar da kwamiticin da zasu gudanar da musabakar a jahar ta Adamawa.
An gudanar da bikin kaddamar wanne a harabar karantar Al Huda dake Bachure dake nan Yola.
Da yake jawabi Hakimin Hong Kuma Danmaliki Adamawa Alhaji Umar Babangida Mahmud Wanda Kuma shine shugaban gidauniyar AYTAM a jahar Adamawa yace AYTAM ta shiryawa marayu gasan ne domin Suma su samu damar shiga a dama dasu a cikin harkokin gasar Karatun Al Qur ani inda yace daga cikinsune za a zabi wadanda zasu wakilci jihar Adamawa a matakin kasa.
Hakimin na Hong ya Kara da cewa za a fara gasar ne daga ran Jumma a 26-7-2024 Wanda Kuma za a kammala a ranan lahadi 28-7-2024.
Da yake bada shawara Dr Aliyu Abdullahi Basullube ya kirayi iyaye da su maida hankali wajen karantar da yaransu ilimin addinin musulunci domin samun yara na gari a tsakanin Al umma.
Itama a jawabinta mataimakiyar amiran AYTAM ta kasa Hajiya Asmau Abubakar yace wannan gasar da za a gudanar shine karo na biyu a jahar Adamawa.
Tace wannan damace ga marayu da Suma zasu nuna nasu basira musammanma a bangaren karatun Al Qur ani Mai girma.
Kwamiticin da aka kaddamar dai sun hada dana Kudi, Saukar da baki, bada Kaututtuka, Abinci, Tsaro, Watsa labarai da dai sauransu.
Comments
Post a Comment