Hukumar Yan Sanda a jahar Adamawa tan tsare da wani matashi da ake zargi da yiwa yar shekaru 12 Fyade.

 




Wani Matashi Mai shekaru 30  ya shiga komar Yan sanda a jahar Adamawa bisa zarginsa da yiwa wata yarinya Mai shekaru 12 da haifuwa.



Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Sanarwan tace Wanda ake zargi Mai Suna Huassaini Salihu ya yaudari yarinyar ne da bata naira dubu 2000. Zuwa gidansa kafin ya gudu amman daga bisani an zakuloshi Wanda a yanzu haka Yan hanun Yan sanda.




Sanarwan ta Kuma baiyana cewa an samu nasaran kama Wanda ake zarginne sakamokon rahoton da aka samu daga mahaifiyar yarinyar.




Kawo yanzu dai Wanda ake zargin ya amsa laifinsa saboda haka za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci sahiriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE