Jami an Yan sanda a jahar Adamawa sun baza komarsu domin kama wasu matasa biyu da ake zargi da kwace waya a karamar hukumar Mubi ta Arewa .

 




Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cika hanu da matasa biyu cikin hudu da ake zargi da kwacen waya a karamar hukumar Mubi ta arewa dake jahar Adamawa.



Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.




Kakakin rundunan yan sandan yace an samu nasaran kama wadanda ake zarginne biyo bayan rahoton da suka samu cewa wasu mutane hudu dake cikin Keken NAPEP sun kwacewa wata maiyiwa kasa hidima Mai Suna Paulina Ayuba wayarta a lokacin da take tafiya a gefen hanya a cikin karamar hukumar Mubi ta Arewa a jahar Adamawa.




Wadanda ake zargin dai sun hada Aminu Aliyu Wanda aka fi Sani da Digashi  Mai shekara 18 da Salisu Muhammed Dan shekaru 18 dukkaninsu mazauna Kasuwar Barkono ne dake Mubi Kuma a yanzu haka ana farautar sauran biyu da suka gudu.




An dai gano waya da Keken NAPEP a wurin wadanda ake zargi saboda haka ana cigaba da bincike domin zakulo wadanda suka bace.



Kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE