Kwamitin mazauna anguwar Dundere sun taya Gwamna Fintiri murnan samun lambar yabo daga fadar shugaban kasa.
Mazauna anguwar Dundere sun taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan karban lambar yabo Wanda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bashi a matsayin gwamnan da yayi fice wajen gudanar da aiyuka a fadin Najeriya.
Shugaban kwamitin Al ummar anguwar ta Dundere Alhaji Muhammed Gwani ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Alhaji Muhammed Gwani yace lambar yabo da aka baiwa gwamnan Ahmadu Fintiri ya dace domin acewarsa gwamna Fintiri ya taka rawan ganin wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar harma da Samar da zaman lafiya a fadin jahar baki Daya.
Alhaji Muhammed ya Kuma baiyana cewa a iya saninsa ba wani gwamna da ya gudanar da aiyukan cigaba a fadin jahar kamar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
Saboda haka nema ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da sukasance masu baiwa gwamna Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya samu damar gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Shugaban kwamitin ya shawarci Al ummar jahar Adamawa da sucigaba da yiwa gwamna Adu o I domin Allah madaukakin sarki ya bashi damar gudanar da aiyukan cigaban.
Ya Kuma baiyana cewa sukam mazauna Dundere a shirye suke sukasance masu baiwa gwamna Fintiri goyon baya a Koda yaushe tare dayi masa Adu o I domin ya samu nasaran gudanar da mulkimsa lafiya ba tare da matsaloliba.
Comments
Post a Comment